Tuesday, 30 April 2019

Ku shirya akwai matsin tattalin arziki dake tunkarar kasarnan>>Gwamna Yari

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yi gargadin cewa a shirya fa akwai matsin tallalin arziki da kasar zata sake shiga nan da tsekara me zuwa, shugaban kungiyar, Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yarine ya bayyana haka.Yari yayi wannan maganane a wajan taron sanin makamar aiki da kungiyar tawa sabbin zababbun gwamnoni da wanda suka zarce a hedikwatarta dake babban birnin tarayya, Abuja, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

Yari ya jawo hankalin gwamnonin inda yace sai sun yi amfani da kwarewa wajan yin mulkinsu da kuma amfani da kudaden da gwamnatin tarayya ke basu yanda ya kamata tunda itace babar hanyar samun kudi ga jihohin, sannan ya gargadi gwamnonin da cewa su zage damtse wajan tarar wata matsalar tattalin arziki dake tunkaro kasarnan nan da shekara me zuwa.

Ya kuma baiwa mayan maikatun dake samar da kudin shiga a kasarnan, irinsu NNPC da Custom da FIRS shawarar cewa sai sun zage damtse wajan aikinsu musamman ganin yanda gwamnatin tarayya ta kara kudin Albashi zuwa dubu 30.

No comments:

Post a Comment