Tuesday, 16 April 2019

Kungiyar kananan kabilun Najeriya sun bukaci Atiku ya fice daga Najeriya ya koma kamaru sannan ya nemi afuwar 'yan Najeriya nan da kwanaki 21

Wata kungiyar kananan kabilun Najeriya ta baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar kwanaki 21 da ya koma kasarshi ta asali watau Kamaru kokuma ya nemi zama dan Najeriya ko su dauki mataki akanshi.Kungiyar ta fitar da sanarwane a ranar Litinin din data gabata ga manema labarai ta hannun sakataren ta, Abdulmuminu Hassan inda sukace koda ogan Atikun, watau Obasanjo dalilin da yasa yaki yadda Atikun ya gajeshi kenan a shekarar 2007. Domin ya bayyana a littafin da ya rubuta cewa, shifa yana tantamar asalin Atikun.

Sannan irin abubuwan da Atikun ya rika yi lokacin yana mataimakin shugaban kasa sun nuna karara aikine irin na me son rusa kasarnan. 

Kungiyar ta kara da cewa, wannan dalilidai na kasancewarshi ba dan Najeriya ba yasa tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB a lokacin mulkinshi ya ki yadda ya baiwa Atiku mukamin shugaban hukumar hana fasa kwauri watau Custom.

Kungiyar ta kara da cewa abin kunyane ga hukumomin Najeriya irin yanda zasu bar haka ta faru na tsawon lokaci ba tare da sun gano ba.

Dan haka sun baiwa Atikun kwanaki 21 da ya koma kasar shi ta asali watau Kamaru sannan kuma ya nemi afuwar 'yan Najeriya ko kuma yana da zabin ya nemi a bashi izinin zama dan Najeriya, idan ba haka ba to zasu mamaye titunan kasarnan da zanga-zanga.

No comments:

Post a Comment