Thursday, 11 April 2019

Likita ya gano tarin kwari a idon wata mata

Wasu likitoci a Taiwan sun gano wasu kananan kwari masu kama da kudan zuma guda hudu a idon wata mata.


Matar mai kimanin shekara 28 da haihuwa wadda aka kira Ms He, ta rika fitar haki daga idanunta bayan da kwarin suka fada idonta.

Daya daga cikin likitocin da suka duba matar, Dr Hong Chi Ting, ya shaida wa BBC cewa, ya kadu matuka bayan ya fito da kwarin hudu daga idon matar.

Bincike ya gano cewa wadannan kwari zafi ke janyo su, kuma idan sun shiga idon mutum su kan sa shi zubar da hawaye sannan kuma su rinka shan hawayen.


Kwarin sun shiga idon matar ne a lokacin da ta ziyarci kaburburan 'yan uwanta inda anan ne ta ga ciyawa ta rufe kaburburan sai ta sunkuya ta na cirewa.

Matar ta ce taji wani abu ya shiga idonta, amma a zatonta ko kura ce, sai kawai ta ci gaba da cire ciyawar da ta ke.

Ta ce bayan wasu 'yan sa'oi, ai idonta ya fara kumbura, sannan kuma sai ta fara jin radadi a idon hakan ya sa ta garzaya asibiti.

Ko da zuwanta likitoci suka dubata, sai suka gano cewa akwai wani abu a idon, daga nan ne aka fara gwaje-gwaje can dai suka hango kafafuwan kwarin.

Likitan da ya ciro kwarin ya ce da haska da wata na'ura ya hango abu kamar kafa kwari, sai ya sa hannu a hankali ya janyo ta ashe kafar daya daga cikin kwarin da suka shiga idonta ne.

Likitan ya ce, ba mamaki iska da kura ne suka haddasa shigar kwarin cikin idon matar, bayan sun shiga kuma sai suka makale a ciki.

Dr Hong Chi Ting, ya ce matar ta auna babban arziki da bata sosa idonta ba a lokacin da ta ji kamar abu ya shigar mata idon, da ta sosa inji shi, da sai kwarin sun shige can cikin idonta.

Likitan ya ce wannan shi ne karon farko da suka samu irin wannan lamari, kuma dukkannin kwarin hudu an ciro su da rai.

Yanzu haka dai an sallami matar da ga asibiti kuma tana samun sauki.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment