Monday, 15 April 2019

Liverpool ta lallasa Chelsea da ci 2-0: Sadio Mane ya kafa tarihi: An bukaci a daina saka 'yan wasa Chelsea 2 a wasa


Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sha kashi a hannun Liverpool a wasan da suka buga ranar Lahadi da ci 2-0. Sadio Mane da Mohamed Salah ne suka ciwa Liverpool kwallayen bayan da aka dawo hutun rabin lokaci.

Saidai a bangaren Chalsea, bayan kammala wasan, magoya bayan kungiyar sun rika yekuwar cewa basa son sake ganin 'yan wasa biyu sun buga musu wasa.

'Yan wasan kuwa sune, Gonzalo Higuain da Willian saboda basu tabuka abin azo a gani ba.

Shi kuwa Mane wannan ne kakar wasa da ya fi zura kwallaye da yawa tun zuwanshi Liverpool inda yanzu yake da yawan kwallaye 21 a dukkanin gasar da ya buga a kakar wasa ta bana, a Firimiya yana da 18.

Liverpool dai ta rike matsayinta na daya akan teburin na Firmiya da wannan nasara data samu.

Hakanan itama Manchester City ta lallasa Crystal Palace da ci 3-1 inda Raheem Sterling yaci mata kwallaye 2 sannan Gabriel Jesus yaci 1.
No comments:

Post a Comment