Wednesday, 10 April 2019

Liverpool ta lallasa FC Porto 2-0

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lallasa FC Porto daci 2-0 a gidanta a wasan Quarter Finals da suka buga da daren jiya, Talata. Naby Keita ne ya fara ciwa Liverpool kwallo sannan sai Roberto Firmino ya ci mata ta biyu.Sadio Mane dai ya ci kwallo bayan dawowa hutun rabin lokaci amma alkalin wasa ya hanata, a haka aka tashi wasan 2-0.

Me horas da kungiyar Liverpool, Jurgen Klopp ya yabawa 'yan wasan nashi da wannan bajinta da suka nuna inda yace sun cancanta su yi nasara a wasan, saidai yace har yanzu suna da jan aiki a gabansu dan sun san ba zasu ji da dadi ba a gidan FC Porto.

No comments:

Post a Comment