Saturday, 6 April 2019

Liverpool ta sake komawa ta daya kan teburin Firmiya

Liverpool ta koma matakinta na daya a kan teburin Premier, bayan da ta doke Southampton da ci 3-1 a wasan mako na 33 da suka yi a St Mary ranar Juma'a.


Southampton ce ta fara cin kwallo ta hannun Shane Long minti tara da fara wasa, yayin da Liverpool ta farke ta hannun Naby Keita saura minti tara su je hutu.

Saura minti 10 a tashi daga karawar Mohamed Salah ya kara na biyu, sannan Jordan Henderson ya ci wa Liverpool kwallo na uku daf hakan ya tabbatar mata da maki uku rigis.


Kwallon da Salah ya ci ya kawo karshen wasa shida bai zura kwallo a raga ba.

Da wannan sakamakon Liverpool ta hada maki 82 ta koma ta daya, ita kuwa Manchester City ta koma ta biyu da maki 80.

A ranar Asabar Manchester City za ta fafata da Brighton a wasan daf da karshe a gasar FA Cup a Wembley, inda City ke fatan lashe kofi hudu a bana.

City ta ci kofin Caraboa na shekarar nan, sannan za ta fafata da Tottenham a wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League.

A ranarv 9 ga watan Afirilu Liverpool za ta karbi bakuncin FC Porto a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar ta Zakarun Turai.

A wasa 33 da Liverpool ta buga a Premier bana ta ci wasa 25 da canjaras bakwai da rashin nasara a karawa daya, sannan ta zura kwallo 75 a raga aka ci ta 20.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment