Wednesday, 17 April 2019

Maganar kara kudin mai da cire tallafin man fetur tana kasa tana dabo

Karamin ministan Mai Ibe Kachiku ya bayyana cewa tana kasa fa tana dabo akan maganar karin kudin man fetur a kasarnan da kuma maganar cire tallafin man gaba daya.A wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na kasa NTA da safiyar jiya, Talata Kachiku ya bayyana cewa, kudin da ake saukar da man fetur din ya dara na wanda ake siyar dashi ga jama'a da Naira 35. Yace hakan ya farune bayan tashin farashin danyen man a kasuwannin Duniya.

Yace a yanzu kudin da ya kamata ana sayar da man shine Naira 180 maimakon 145 kuma idan ya kara tashi sama da haka nan gaba to lalai kasar zata iya talaucewa.

Yace a shekarar 2016 lokacin da za'a kara kudin mai sun zauna da kungiyoyin kwadago inda duka suka amince da karin saidai daga baya sauran kungiyoyin sun fice sai na ma'aikatan man fetur din kawai aka bari amma da yake mutane sun fahimci abinda ke faruwa sai ba'a samu matsala ba.

Yace kungiyoyin kwadago a koda yaushe suna bayar da hadin kai wajan cire tallafin mai, abinda dai kawai suke tambaya shine me za'ayi da kudin tallafin idan aka ciresu?

Ya kara da cewa bisa rahoton hukumar dake kula da farashin man fetur a Najeriya za'a rika sayar da man ne akan Naira 189 saboda tashin da man yayi a kasuwar Duniya zuwa dala 66 kowace ganga.

Yace tun a shekarar 2017 shugaban kamfanin mai na kasa ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na fuskantar matsin lamba akan ta kara kudin mai zuwa 171.4 saboda tashin da danyen man yayi a zuwa dala 64 kowace ganga.

Kachiku ya kara da cewa yanzu fa kamfanin mai na kasa NNPC ne kadai ke shigo da mai kasarnan kusan tsawon shekaru 2 kenan tun bayan da 'yan kasuwa masu zaman kansu suka janye daga shigo da man.

Sannan har yanzu akwai kudin tallafin da 'yan kasuwar ke bin gwamnati da bata biya su ba.

Yace amma maganar gaskiya idan aka tsaya aka duba za'a cewa kashi 80 na mutanen Najeriya basu bukatar tallafin man fetur din. Dan haka maganar cire tallafi tana bukatar a kula da ita sosai ne kawai da kuma yanda za'a isarwa da mutane labarin.

Yace akwai kuma maganar gyara matatun man kasarnan wanda ya kamata ayi shi ta kowane hali, koda ma ace 'yan kasuwane za'a baiwa wanda yace shi a ganinshi a baiwa 'yan kasuwar ma yafi dacewa.

No comments:

Post a Comment