Friday, 12 April 2019

Mahaifiyar Firaministar Jamus ta rasu

Firaministar Jamus Angela Merkel ta rasa mahaifiyarta mai shekaru 90 Herlind Kasner.


Labaran da jaridun Jamus suka fitar sun rawaito kakakin gwamnati Steffen Seibert na cewar mahaifiyar Firaminista Merkel mai suna Herlind Kasner inda ya ce, suna mika sakon ta'aziyya ga Shugabar da iyalanta.

Ba a bayyana yaushe ne Herlind Kasner ta mutu ba, ama jaridun Jamus sun ce, ta mutu a farkon wannan wata.

An bayyana cewar za a yi mata Jana'iza a kwanaki masu zuwa.

A shekarar 2011 ne mahaifin Angela Merkel Pasto Horst Kasner ya mutu.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment