Thursday, 11 April 2019

Majalisar Tarayya ta bayyana hanyar da za'a magance matsalar tsaron kasarnan

Majalisar dattijai ta bayyana hanyar samar da 'yansandan jihohi a matsayin wadda zata kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita a kasarnan. Majalisar ta dauki wannan matakinne bayan da Sanata Kabiru Marafa da Sanata Emmanuel Bwacha suka kawo korafe-korafe akan lamarin 'yan bindiga da suka addabi yankin Arewa maso yamma.Majalisar ta kuma bukaci da a ware Biliyan 10 dan tallafawa wadanda lamarin hare-haren Zamfara ya rutsa dasu sannan ta yabawa 'yan Najeriya da suka fito suka nuna damuwa akan halin da mutanen Zamfara ke ciki.

No comments:

Post a Comment