Saturday, 13 April 2019

Man U ta ci West Ham 2-1: Pogba ya kafa tarihi

Manchester United ta lallasa West Ham da ci 2-1 wanda dukansu Pogbane yaci matq da bugun daga kai sai gola.A yanzu dai Pogba nada kwallaye 15 kenan a gaba dayan gasar da yake bugawa sannan yana da kwallaye 12 a gasar Firimiya, ya kuma bayar da taimako anci kwallaye 22 a wannan kakar 

Yanzu dai Ruud van Nistelrooy ne kawai ya fi Pogba ciwa Man U kwallaye ta bugun Penalty inda yake da kwallaye 8 Pogba kuma nada 7.

Wannan nasara ta sa Man U ta koma ta 5 a kan teburin firimiyar.

kocin West Ham, Pellegrini ya bayyana cewa dandai kawai babu na'aurar nan ne ta taimakawa alkalin wasa amma da sune zasu yi nasara a wasan.

Hakanan shima kocin Man u, Ole Gunnar ya bayyana cewa, a wasan na yau kam gaskiya sa'a kawai suka taka dan West Ham ta fisu buga wasa da kyau.

Hakanan Tottenham, duk da Kane baya nan, ta lallasa, Huddersfield Town da ci 4-0 wanda Lucas Moura ya ci kwallaye 3 Wanyama kuma ya ci 1. Wannan nasara tasa suka koma matsayi na 3 a kan teburin firimiya.


No comments:

Post a Comment