Monday, 15 April 2019

Manchester United ta saka Yuro miliyan 150 a matsayin kudin sayar da Pogba


Rahotanni sun bayyana cewa,kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta gayawa wakilin Pogba cewa ba fa zata sayar da dan wasan cikin sauki ba.

A takaice ma tana so ta tsawaita kwantirakinshi zuwa shekarar 2021 domin tunda tsohin me horas da kungiyar, Jose Mourinho ya tafi to Pogba be da matsala da kungiyar.

Saidai kuma akwai rahotannin dake cewa shi Pogban yana son komawa Madrid dan ya buga mata wasa.

Manchester United tace idan Madrid na son sayen Pogba to saita biyata Yoru Miliyan 150.

Da dama dai na ganin wannan kora da halice Man U din kewa Real Madrid akan cinikin Pogba.

No comments:

Post a Comment