Wednesday, 10 April 2019

Manchester United ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Barca: Bayan kammala wasan an bukaci kocin Man U din ya sayar da wani dan wasa

Kwallon da Luke Shaw yaci kansu ce ta baiwa Barcelona nasara a wasan da Manchester United ta buga dasu na neman cin kofin Champions League a daren yau, Chris Smalling ya jiwa Messi rauni a fuska inda har ya zubarmai da jini.
Bayan kammala wasan, magoya bayan Manchester United sun yi kira ga me horas da kungiyar, Ole Gunnar Solskjaer daya sayar da Ashley Young saboda shirmen da yayi a wasansu na yau din.

Gididdiga dai ta bayyana cewa, Young ya bugo kwallaye 11 daga bangarenshi wadda daga cikin babu ko daya data samu dan wasan Manchester United.

Wannan yasa bayan kammala wasan magoya bayan Man U suka shiga shafukan sada zumunta inda suka rika kira da a sayar da dan wasan.

No comments:

Post a Comment