Thursday, 11 April 2019

Marafa yawa Saraki tallar auren wata mata da tace tana sonshi

A zamanta na ranar Alhamis, majalisar dattijai ta samu labarin godiyar jama'ar mazabar sanata Kabiru Marafa me wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya bisa amincewa da ware Naira Biliyan 10 dan tallafawa mutanen jihar da hare-haren 'yan bindiga ya rutsa dasu.Da yake magana a zaman majalisar, Marafa ya bayyana cewa mutanen mazabarshi sunce a mikawa majalisar dattijai da shugabanta Bukola Saraki godiya ta musamman bisa amincewa da wadannan zunzurutun kudi dan tallafa musu. 

Marafa ya kara da cewa akwai wata mata a mazabarshi data bashi sako na musamman tace ya mikawa shugaban majalisar, Bukola Saraki, tace tunda take bata taba ganin Sarakin ya buga gudumarnan tashi da karfi ba kamar jiya, dan haka idan ya tafi hudu ta bayar da kanta gareshi idan yana da bukata ya aureta.

Marafa yace idan ya kalli gidan Bukola Sarakin yakan ga cewa akwai gurbin da ya kamata a cike dan haka ya duba wannan tayi, yace duk da yana girmama uwargidan Sarakin amma daga inda ya fito mutun na iya auren mata har 4.

No comments:

Post a Comment