Saturday, 6 April 2019

Messi da Ronaldo sun zo kankankan a yawan kwallaye

A wasan da ta buga da Villarreal ranar Talatar data gabata, Barcelona ta tashi wasan 4-4 wanda aka sha gumurzu sosai, tauraron dan wasanta, Lionel Messi wanda ba'a fara wasan dashi ba amma daga baya da gumu yayi gumu aka sakoshi ya ci kwallo daya daga bugun tazara.Wannan kwallon da ya ci ta zama kwallo ta 414 da ya ci a duk wata gasar kungiyoyi daya taba bugawa.

Wannan yawan kwallo daya samu sun zo daidai dana abokin takararshi,Cristiano Ronaldo wanda shima yana da kwallaye 414 da ya ci a dukkanin gasar kungiyoyi daya buga wanda suka hada da, guda 84 daya ci a gasar Firimiya da guda 311 da ya ci a gasar Laliga da kuma 19 da yaci a gasar Seria A.

Su biyunne dai kawai suka taba kaiwa ga wannan mataki na cin kwallaye mafi yawa a dukkanin gasar kwallayen nahiyar turai biyar da ake bugawa.

No comments:

Post a Comment