Tuesday, 30 April 2019

Messi naso Barcelona ta sayo tauraraon Manchester United


Rahotanni sun bayyana cewa, tauraron dan kwallon Barcelona, Lionel Messi na fatan ganin kungiyar tashi ta sayo gwanin Manchester United, Marcus Rashford saboda dan wasan yana birgeshi kuma zai so yayi wasa tare dashi.

Don Balon ta ruwaito cewa matashin dan wasan zai iya zuwa Barca ne a matsayin shirin da kungiyar take na samun madadin Luis Suarez.

Kwantirakin da Rashford ya sawa hannu na bugawa Man U wasa zai karene a kakar wasan badi, kuma Man U din na da damar sake rikeshi har na tsawon karin shekara daya kamar yanda yake a sharadin kwatirakin amma ana ganin cewa dan wasan zai so komawa Barca ko dan ya samu damar cin Champions League, lura da cewa Man U da wuya su je gasar ta badi, sannan son da Messi yake mai zai kara saukakamai zuwa kungiyar.

No comments:

Post a Comment