Saturday, 6 April 2019

Messi ne gwarzon La Liga na watan Maris

Hukumar gudanar da gasar La Liga ta bayyana dan kwallon Barcelona, Lionel Messi a matsayin wanda ya fi yin fice a watan Maris a gasar.


Messi kyaftin din Barcelona ya ci kwallo shida a wasa hudu da ya kara a La Liga a watan Maris, inda ya ci Rayo Vallecano da Betis da kuma Espanyol.

Za a bai wa Messi lambar yabon a Camp Nou kafin fafatawar da Barcelona za ta yi da Atletico Madrid a gasar La Liga wasan mako na 31 a ranar Asabar.


Atletico ta tashi 1-1 da Barcelona a wasan farko a kakar bana ta La Liga ranar 24 ga watan Nuwambar 2018.

Lionel Messi ya ci wa Barcelona kwallo 32 shi ne kan gaba a gasar La Liga, sai Luis Suarez na Barcelona na biyu da ya ci 19, sannan Stauni na Girona mai 17 a raga.

Barcelona tana mataki na daya a kan teburi da maki 70, yayin da Atletico Madrid ce ta biyu da maki 62.

Kungiyar ta Spaniya za ta ziyarci Old Trafford domin buga gasar Champions League karo na farko da za su yi a kakar bana 10 ga watan Afririlu
BBChausa.

No comments:

Post a Comment