Tuesday, 16 April 2019

Mourinho ya fadi yanda sakamakon wasan Champions League na yau zai kasance

Tsohon me horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho yayi kintacen kungiyar da yake ganin zata samu nasara a wasan da za'a buga yau na neman cin kofin Champions League tsakanin Manchester United da Barcelona da kuma tsakanin Juventus da Ajax.Da yake magana da RT, Mourinho yace, yana ganin Manchester United ce zata ci Barcelona sannan kuma Ajax ce zata fitar da Juventus.

Barcelona dai nada kwallo daya a ragar Manchester United a wasan da suka buga a makkn daya gabata da suka taci 1-0. Hakanan Juventus na da kwallon waje a wasan da suka buga a Ajax a makon daya gabata wanda suka tashi 1-1.

Mourinho ya kara da cewa duka kungiyoyin da suka kai wannan matsayi babu wadda ba zata iya cin 'yar uwarta ba amma yana ganin Juventus da Barcelona za'a fitar.

No comments:

Post a Comment