Monday, 15 April 2019

Muna kan hada sunayen mutanen da hare-harenku suka kashe>>Sarakunan Zamfara suka gayawa sojoji

Kungiyar sarakunnan jihar Zamfara ta mayarwa da hukumar soji martanin cewa a shirye take ta bayyana sunayen jama'ar da basu ji ba basu gani ba da harin da suka kai ta sama suka kashe maimakon 'yan ta'addar da ake hari.Maigana da yawun sarakunan jihar, Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru yace yanzu haka suna kan tattara sunayen mutanen da harin na sojoji ya kashe wanda ba 'yan bindigar bane kuma nan gaba zasu bayyana su. Ya kara da cewa sunaye da kuma yawan 'yan bindigar da sojin sukace sun kashe kirkirarsu kawai suka yi, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Tun farko dai sarakunan Zamfarar ne suka fara bayyana cewa harin na sojin baya kaiwa ga maboyar 'yan bindigar, mutanen da basu jiba basu gani ba suke kashewa inda suka bayar da shawarar kawo sojoji wajan da 'yan bindigar ke boye.

Hukumar sojin dai ta karyata wancan ikirarri inda tace bata kai hari sai ta tabbatar da akwai 'yan bindigar sannan ta bukaci sarakunan su fadi wanda aka kashe idan da gaske suke.

No comments:

Post a Comment