Monday, 15 April 2019

'Mutum be bukatar takardar sakandire kamin ya zama shugaban kasa ko gwamna'

Babban lauya wanda ya kuma yiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari yakin neman zabe a zaben shugaban kasar daya gabata, Festus Keyamo ya tabbatar da cewa mutum baya bukatar takardar WAEC kamin ya zama shugaban kasa ko kuma gwamna.Festus Keyamo ya bayyana hakane a shafinshi na Twitter inda yace, takardar kammala makarantar Firamare kawai ake bukata sai kuma iya rubutu da karatun Turanci yanda mutun zai gamsar da hukumar zabe shikenan.

Wannan lamari ya jawo cece-kuce inda wasu suka rika taso da maganar takardar kammala makarantar Sakandire ta shugaba Buhari da aka yi a baya saidai Festis Keyamo ya sake jaddada wannan magana tashi yace tana cikin kundin tsarin mulki.


No comments:

Post a Comment