Sunday, 7 April 2019

Na taba ciro dala miliyan 10 daga banki dan kawai in tabbatarwa da kaina cewa ni me kudine>>Dangote


Image result for dangote
Attajirin da ya fi kowane bakar fata kudi a Duniya, Alhaji Aliko Dangote ya bayar da labarain yanda ya taba fitar da zunzurutun kudi har dala miliyan 10 dan kawai ya tabbatarwa da kanshi cewa lallai shi me kudine da gaske.

Dangotenne da kanshi ya bayar da wannan labari a wajan taron Mo Ibrahim da aka yi a birnin Abidjan na kasar Kwadebuwa a jiya Asabar. Anga Dangoten na wannan bayanine a cikin wani hoton bidiyo da aka wallafa a shafin Youtube na Gidauniyar Mo Ibrahim din.

Yace, idan mutum ya fara kasuwanci, burinshi na farko shine ya ga ya samu miliyan daya a matsayin riba, kuma na samu hakan. injishi.

Ya kara da cewa, da na tsaya na duba sai naga duk kudin da ake cewa ina su a takardane kawai. Shiyasa wata rana na tashi takanas.. naje banki, lokacin ba dokar data ka'ide yawan kudin da mutum zai iya cirewa, na cire dala miliyan 10 daga asusun ajiyata, na saka a bayan mota, na tafi dasu gida.

Dangote ya kara da cewa da naje gida sai na sakasu a gaba ina kallo, na gayawa kaina cewa lallai yanzu na yadda inada kudi. Yace washe gari ya mayar da kudin banki.No comments:

Post a Comment