Wednesday, 10 April 2019

Nafisa Abdullahi ta shiga gaba wajan yin Allah wadai da abinda Hadiza Gabon ta wa Amina Amal

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta fito karara ta nuna rashin jin dadinta akan dukan da Hadiza Gabon tawa Amina Amal bisa zargin bata mata suna da kazafin Madigo, Nafisar tace, ba ruwanta da abinda ya hadasu amma ita dukan da akawa Aminar ne bata goyon baya.Ta yi rubuce-rubuce da yawa kamar haka:

Nafisar tace ba zata taba goyon bayan cin zarafiba ballan tana idan taga ana rainin wayau. Tace, ina kamun kan da nutsuwa da kikewa nunawa Duniya cewa kina dashi, ina kirkin da kike nunawa Duniya cewa kina dashi? a hakane zaki tabbatar da gaskiyarki ta hanyar cin zarafinta?  Da ace kowa irin wannan hanyar yake bi wajan neman hakkinshi da kema baki tsira ba, saboda ba zaki so a miki haka ba ko wannan ba zai sa ki sassauta ba? Ke kina son ki kare mutuncinki amma ita kin sakata a Idon Duniya kina cin nata mutuncin, shin wama ya baki damar dukan mace 'yar uwarki, saboda kina ganin cewa ita ba komai bace ba? Wasu mutanen na rayuwar karya amma basu sani ba cewa abinda suke aikatawa yana nunawa Duniya ainihin kalarsu.

Ta kara da cewa duk me cin mutuncin wani/duka yana jin dadi to mutumin banzane azzalumi, kuma ban zargi kowa ba sai ita data maida kanta banza bata rike kimar kanta ba, ita data dauka mutum ake kaiwa kuka ba Allah ba.

Wani dai ya bukaci a bashi lambar Amina Amal din saboda yana bukatar yayi magana da ita saboda wannan abun daya faru da ita cin zarafin wanda aka fi karfine.

Nafisar tace tabbas hakane, da taso ta wanke kanta da saita ce mata taje inda ta yi wancan rubutu ta karyata kanta, shin ma wai me ya kawo wannan cin zarafi? Saboda ita dai bata ambaci sunan kowa ba.

Nafisar dai tace, Wannan abinda ta yi wa yarinyar ai kara daukaka sunanta ta yi ba tare da ta sani ba.

Saidai wani ya tambayi Nafisar cewa anya wadannan surutan da take babu wata jikakka tsakaninta da Hadizar?

Ita kuwa ta bashi amsar cewa ko daya, ita da Hadiza basu da matsala tsakaninsu,kawai dai dukan da akawa yarinyarne bai kamata ba kuma gaskiyace dole a fadeta.
Wata dai ta tambayi Nafisar cewa shin wai da gaskene itama Hadiza Gabon ta taba mata shegen duka?

Nafisar ta bata amsar cewa sun wa juna dai, Hadizar ta taba shammatarta ta dake ta, itama kuwa ta shammace ta ta rama, dan haka sunwa juna shegena duka dai.

Saidai tace sun warware waccan matsala tun shekarar 2017
Wani ya tambayi Nafisa shin wai idan itace akawa wannan abu ba zata dauki matakin daya kamata dan kare mutuncinta ba?

Saidai ta bashi amsar cewa babu irin sharri da kazafain da ba'ayi ba amma kowa nada yanda yake warware matsalolinshi, ita dai bata yadda da hanyar duka ba.

Ta kuma kara da cewa,  Abinda ta yi ya nuna cewa ta dawo da kanta matsayi daya da yarinyar ko kumama kasa da ita.


No comments:

Post a Comment