Wednesday, 17 April 2019

Najeriya tafi samun tsaro yanzu fiye da shekarar 2015>>Lai Muhammad

Ministan watsa labarai, Lai Muhammad ya tabbatar da cewa a yanzu Najeriya ta fi samun zaman lafiya fiye da shekarar 2015.Da yake magana akan hare-haren 'yan bindiga a jihar Zamfara da sauran wasu jihohin kasarnan,Lai Muhammad yace gwamnati na bakin kokarinta wajan ganin ta kawo karshen lamarin.

Da yake magana akan zabe kuwa yace shugaba Buhari ne dama ya cancaci cin zaben sannan yayi nasara a zaben da aka yi bisa gaskiya.

No comments:

Post a Comment