Tuesday, 16 April 2019

Ole Gunnar Solskjaer: 'Na kalli kwallon da na ci a Camp Nou kusan sau miliyan'

Ole Gunnar Solskjaer zai koma filin wasa na Camp Nou a karon farko cikin shekara 20 tun bayan kwallo mai cike da tarihi da ya ci a filin wasan.


A wata hira da ya yi, ya tuna kwallon da ya ci Bayern Munich a filin wasan na Camp Nou a shekarar 1999, wadda ta bai wa United nasarar lashe kofin Zakarun Turai na Champions League.

Tuni tawagar Man United ta isa birnin Barcelona, inda a yammacin ranar Talata za su kara a wasa na biyu na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turan ta Champions League.

Barcelona ce ta yi nasara a wasan farko da ci 1-0.

Solskjaer ya ce: "Na kalli kwallon nan kusan sau miliyan don shi ne daren da ba zan taba mantawa da shi ba, amma kar ka gaya wa mai dakina fa."

"Mutane da yawa sun kira ni a lokacin don su taya ni murna," in ji Solskjaer.


Dwight Yorke yana cikin 'yan wasan da suka buga wasan tare da Solskjaer, kuma ya shaida wa BBC cewa dama suna da kwarin gwiwar farke kwallon.

"Muna da kwarin gwiwar za mu farke saboda da ma ba mu taba tunanin za a cinye mu da 0-1 ba."
BBChausa.

No comments:

Post a Comment