Monday, 1 April 2019

Pogba zai ci gaba da zama a United>>Solskjaer


United
Ole Gunnar Solskjaer ya ce Paul Pogba zai ci gaba da murza-leda a Manchester United a badi, bayan da ake rade-radin cewar zai koma Real Madrid.


Pogba ya ce Real kungiya ce da kowanne dan kwallo ke mafarki ya yi wa tamaula a makon jiya, inda Zinedine Zidane ya ce yana kaunar dan wasan tawagar Faransa mai shekara 26.

Sai dai kuma Solskjaer ya ce ''Pogba ya fadi albarkacin bakinsa da cewar kowa na son buga wa Real Madrid kwallo, saboda haka komai a fayyace yak''.
Pogba ya koma United daga Juventus a 2016 kan fam miliyan 89 a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya, sai dai ya ci karo da koma baya kan makomarsa a Old Trafford a farkon kakar bana.
Dan kwallon tawagar Faransa ya samu rashin jituwa karo da dama da koci Jose Mourinho, wanda United ta sallama a watan Disambar 2018.
Kawo yanzu Pogba ya ci kwallo tara karkashin Solskjaer, wanda ya ce zai gina United a badi kan kokarin dan wasan na Faransa da yake yi a kungiyar.
A ranar Talata United za ta fafata da Wolverhampton a wasan mako na 33 a gasar Premier, kuma Solskjaer ya tabbatar cewar Romelu Lukaku ya murmure.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment