Tuesday, 2 April 2019

Ramos zai fito a fim din Game of Thrones

Shafin 90mins ya ruwaito cewa, tauraron da kwallon kafar Real Madrid, Sergio Ramos zai fito a shahararren fim dinnan na kamfanin HBO, watau Game of Thrones kashi na karshe da zai fito a cikin watannan.90mins yace ya samu wasu labaran sirrine da suka bayyana mai haka saidai ba'a bayyana ko a wane bangare na fim din Ramos zai fito ba. Amma sun kara da cewa anga Ramos din sanye da  kayan sulke na yaki, rike da takobi yana atisaye tare da wasu taurarin fim din.

Koma dai menene lokaci zai bayyana.

No comments:

Post a Comment