Sunday, 7 April 2019

Ranar dana fara ganin Ronaldo na ji ina sonshi>>Georgina Rodriguez

Budurwar tauraron dan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, watau Georgina Rodriguez ta bayyana yanda suka hadu a shekarar 2016 inda tace ranar da ta fara ganinshi ta ji tana sonshi.



Georgina ta bayyana cewa sun fara haduwa da Ronaldonne a wajan sayar da kayan Gucci inda basu yi wata magana me tsawo ba.

Tace bayan kwana biyu sai suka sake haduwa a wajan wani taron, a nanne muka samu lokacin da muka yi magana ta fahimta, kuma dukan mu mun kamu da son juna a ranar farko da muka hadu, injita.

Georgina dai ta haifamai diya kuma tana kula da sauran 'ya'yanshi.

No comments:

Post a Comment