Sunday, 7 April 2019

Ronaldo na dab da daukar kofin Seria A bayan barin Madrid

Juventus ta samu nasarar doke AC Milan a wasan hamayya da suka fafata a filin wasa na Allianz Stadium da ke birnin Turin.


Wannan sakamako zai bai wa Juve damar lashe kofin idan Napoli ta yi rashin nasara a hannun Genoa a ranar Lahadi, wanda kuma shi ne na takwas a jere.

Kuma hakan na nufin saura kasa da sa'o'i 24 Cristiano Ronaldo ya dauki kofin lig Seria A a karon farko a rayuwarsa, kari a kan Premier da kuma La Liga da ya dauka a baya.

Ronaldo ya bar Real Madrid a karshen kakar bara bayan da ya lashe kofin Zakarun Turai sau uku a jere.

Duk da cewa dan wasan mai shekara 33 bai buga wasan hamayyar ba, ana ganin shi ne kan gaba wajen taimaka wa Juve a kakar bana.

Kwallaye 19 ya ci wa Juventus a gasar ta Serie A a bana, kuma ya taimaka wajen cin guda 8.


AC Milan ce ta fara zura kwallo a wasan, inda dan wasanta Krzyszt ya daga ragar Juve kafin zuwa hutun rabin lokaci, to amma bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci Paulo Dybala ya farke kwallon da bugun fenareti.

Sai dai kuma ana saura minti shida a tashi daga wasan dan wasa Kean, wanda magoya bayan kungiyar suka nuna wa wariyar launin fata a wasan da suka yi ranar Laraba da kungiyar Cagliari, ya zura kwallon da ta bai wa Juventus nasara a wasan.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment