Thursday, 25 April 2019

Ronaldo na so Juventus ta siyo tauraron Barcelona

Bayan fitar da Juventus daga gasar cin kofin zakarun turai, tauraron dan kwallonta, Cristiano Ronaldo na so kungiyar ta yi canje-canje da sayen 'yan wasa saboda kakar wasa me zuwa. Duk da cewa Juve ta lashe kofin Seria A amma ba haka nan taso ba.Fox ta ruwaito cewa Ronaldo ya bukaci Juve ta sallami me horas da 'yan wasanta na yanzu, Max Allegri sannan ta sayo kocin Manchester City kuma tsohon tauraron kocin Barcelona, Pep Guardiola a kakar wasa me zuwa. Duk da cewa Max Allegri ya ce bashi da shirin barin Juve amma watakila idan wannan magana ta tabbata bashi da zabi.

Pep da Ronaldo a baya sun samu rashin jituwa  amma ana ganin cewa idan suka hadu kasancewarsu duk kwararrune a fannoninsu zasu iya bayar da sakamakon da ake so.

Hakanan ana ganin cewa rashin tsari me kyaune na Max Allegri wajan horaswa ya fitar da Juve daga gasar ta Champions League, lura da cewa suna da kwararrun 'yan kwallo.

No comments:

Post a Comment