Tuesday, 23 April 2019

Ronaldo ne na 2 a nahiyar turai da be iya buga free-kick ba

A zaman da Ronaldo yayi a kungiyar Juventus, duk da cewa ya kafa tarihi kala-kala amma burin kungiyar shine ya taimaka mata wajan ciwo kofin Champions League da ta dade bata dauka ba. Saidai ya zuwa yanzu wannan mafarki na su ya kare a kakar wasan bana bayan da Ajax ta ciresu daga gasar.Hakanan Atlanta ta cire Juventus daga gasar Coppa Italiya. Saidai Juventus din a bangare daya kuma ta lashe gasar Seria A sau takwas kenan a jere, duk da cewa wasu na ganin Ronaldo fa shi kadai ba zai iya bayar da abinda ake so ba amma wasu na ganin cewa be cimma burin da kungiyar ta siyoshi saboda shi ba.

Yanzu dai wata kididdiga da SofaScore ta wallafa ta bayyana cewa, Ronaldo ne dan kwallo na biyu wajan rashin iya buga kwallon Free-kick a kaf nahiyar turai inda na daya shine Camillo Ciano, sun samu wannan matakine kasancewar a kakar wasan bana basu ci kwallo ko daya da bugun Free-kick ba.

No comments:

Post a Comment