Sunday, 28 April 2019

Ronaldo ya zarta Messi a yawan kwallayen da suka ciwa kungiyoyinsu

A wasan da Juventus ta buga jiya da Inter wanda suka tashi kunnen daki 1-1, tauraron dan kwallon Juve din, Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin cin kwallaye har 600 wa kungiyoyin kwallon kafa daya bugawa wasa jimulla.Bayan da aka dawo hutun rabin lokacine cikin mintina 62 da wasa, Ronaldo ya farke kwallon da Nainggolan ya cisu, wanna yakai yawan kwallayen da ya ciwa kungiyoyin Sporting CP, Manchester United, Real Madrid da Juventus 600.

Hakan na nufin Ronaldo ya zarta babban abokin takararshi, Lionel Messi a yawan kwallayen da 'yan wasan suka ciwa kungiyoyinsu, yayin da Messin ke da yawan kwallaye 597.


No comments:

Post a Comment