Tuesday, 2 April 2019

Ronaldo zai yi jinyar sama da makwanni 6

Rahotanni daga kasar Italiya sun tabbatar cewa tauraron dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo, zai jinyar makwanni takwas, kafin dawowa wasa.A karshen watan Maris da ya gabata, Ronaldo yasamu rauni a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin nahiyar Turai, da kasarsa Portugal ta buga da Serbia, wanda suka tashi 1-1.

Hakan na nufin Ronaldo ba zai damar buga wasanni biyu da Juventus za ta fafata da Ajax ba a zagayen kwata final na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Zalika Ronaldo ba zai buga wasanin gasar Seria A da Juventus za ta fafata da kungiyoyin Cagliari, AC Milan, SPAL, Forentina, Inter Milan, Torino, AS Roma, Atalanta da kuma Sampdoria ba.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment