Thursday, 11 April 2019

Ruwan bama-baman da ake yi ta sama a Zamfara bayin Allahn da basu ji ba basu gani ba yake kashewa maimakon 'yan bindiga>>Inji Sarakunan gargajiya

Kungiyar sarakunan gargajiya ta jihar Zamfara ta jawo hankalin cewa ruwan wutar da jiragen yakin sojin Najeriya ke yi mutanen da basu ji basu gani ba ake kashewa maimakon 'yan bindigar da ake tsammani.Sarkin bungudu, Alhaji Hassan Attahiru ne ya bayyana haka a ranar Alhamis bayan taron gaggawa da kungiyar sarakunan jihar ta yi wanda ya samu halartar duk sarakunan dake jihar kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito.

Sanarwar bayan taron ta ci gaba da cewa rahotannin da aka samu daga kauyukan, Mutu dake Gusau da karamar hukumar Tsafe da Tangaram a karamar hukumar Anka da Dumburum a karamar hukumar Zurmi dadai sauran wasu guraren da aka yi luguden wuta ta sama an kashe bayin Allahne da basu jiba basu gani ba dan ba maboyar 'yan bindigar bane.

Sanarwar ta kara da cewa samun nasarar wannan yaki da 'yan bindigar da ake yi shine a gano maboyar su sannan a zuba jami'an tsaro a gurin dan yanke duk wata ma'amala tasu.

Sanarwar ta kuma bukaci ministan tsaro daya fito ya bayyana sunayen sarakunan gargajiyar da yace suna taimakawa 'yan bindigar ko kuma ya janye wannan ikirari nashi, ta kara da cewa kawai ministan yana so yayi amfani da sarakunan gargajiyane ya dora musu laifin gazawar jami'an tsaro na shawo kan lamarin.

Sanarwar ta kara da cewa sarakunan ba zasu taba baiwa wani dake da hannu a wannan lamari kariya ba kuma sun jima suna baiwa jamj'an tsaro hadin kai wajan kawo karshen wannan lamari

No comments:

Post a Comment