Tuesday, 16 April 2019

Sammu Aka Yi Wa Buhari, Domin Buharin Da Nake Gani Yanzu Ba Shine Wanda Na Sani A Baya Ba>>Sarkin Gwandu

Alhaji Mustapha Haruna Jokolo, ya yi zargin cewa, sammu ‘Cabal’ suka yi wa Buhari don su ji dadin juya shi yadda suka ga dama.


A hirarsa da sashen Hausa na rediyon Faransa (RFI), Jokolo ya ce, Buharin da yake gani yanzu, ba wanda ya sani ba ne a baya.

“Na yi aiki da shugaba Buhari sau biyu, lokacin yana Gwamnan Arewa maso Gabas da kuma lokachin da yake Shugaban Kasa, na san ba rago ba ne wajen al’ammurra da tafiyar da mulki, amma ka sani fa Manzon Allah (SAW) ma sammu ya kama shi, wadannan mutanen sun yi wa Buhari sammu. Su wadannan ‘yan ‘Cabal’ din nan da ake fada sun yi masa miyagun abubuwa da za su rika juya shi. Ba Buharin da na sani ba ne,” ya jadadda.

Jokolo, ya jawo hankalin Shugaban kasa ya fahimci irin wannan tuggun da ake masa, wanda har matarsa ta yi masa nuni a kansu, kuma yana karanta jaridu, yana sauraron rediyo. “Tunda ya yi rantsuwa da Alkur’ani, ya san sauran in bai sauke hakkin mutane ba”, in ji shi.

Sarkin Gwandu, ya nuna mamakinsa matuka dangane da kalaman Ministan Tsaro, Alhaji Mansur Dan Ali, wanda ya zargi Sarakuna da hannu a kashe-kashen da ake yi a Zamfara.

Ya ce wajibi ne Ministan ya fito ya bayyana sunayen Sarakunan da ake zargi da hannu a rikicin, kuma a kama su a hukunta su tunda ba wanda ya fi karfin doka.

Ya nuna damuwa matuka kan yadda Gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari ya kasa sauke nauyin da aka dora masa na kula da rayuka da dokiyoyin jama’a, ya je ya tare a garinsu Mafara.

Jokolo, wanda tsohon soja ne, ya nuna damuwa da kamun ludayin sojojin da aka tura don kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Zamfara.

Haka nan yanuna damuwa karara akan yadda ake Wulakanta AlQur'ani Mai Tsarki, inda ya bayyana cewa ansamu wasu rahotanni da suke nuna an samu warkokin Alkur'ani a bayan gida ko cikin najasa, yace babu yadda za a zauna lafiya.
Rariya.


No comments:

Post a Comment