Sunday, 21 April 2019

Shagalin bikin tauraron me fadakarwa a Twitter ya jawo cece-kuce

Bayan da hotunan shagalin auren tauraron me fadakarwa a dandalin Twitter, Mustafa wanda aka fi sani da Angry Ustaz suka bayyana, da dama sun yi sharhi akai inda wasu suka zargeshi da aikata abinda yake kiran mutane da su guji aikatawa, lamarin yayi kamari har ya zama daya daga cikin abubuwan da aka fi tattaunawa akansu a Twitter.Wasu sun zargi Mustafa da cewa a baya yana kira da gujewa yin shagalin aure na fariya da kuma yanda wasu amare ke shigar dake nuna surar jikinsu, amma gashi shima yayi. Wasu kuwa sun fito suka kareshi da cewa shima fa dan adam ne kamar kowa kuma zai iya yin kuskure.

Tuni dai Mustafa ya fito yayi godiya ga wadanda suka tayashi murnar aure sannan ya bayyana cewa har yanzu yana nan kan bakanshi na kira a gujewa abubuwan da basu dace ba koda kuwa shima ya aikata hakan.

Karanta ra'ayoyin wasu mutane akan wannan lamari.

No comments:

Post a Comment