Sunday, 14 April 2019

Shugaba Buhari ya nemi hadin kan kasashen Afrika wajan magance kwarar makamai zuwa Najeriya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan jiya a wajan taron kasashen yankin Sahel Sahara wanda ya faru a birnin N'Djamena dake kasar Chadi inda takwarorinshi na Nijar da Togo da sauran wakilan kasashe membobin kungiyar suka halarta.A jawabin da ya gabatar a wajan taron, shugaba Buhari ya nemi handin kan kasashen Afrika wajan maganin kwararar kananan makamai zuwa Najeriya wanda ke karewa a hannun masu  tada kayar baya.

Ya kuma bukaci baiwa 'yan Najeriya dake zaune bisa ka'aida da wanda ma basa zaune bisa ka'ida a kasar Libya.


No comments:

Post a Comment