Friday, 5 April 2019

Shugaba Buhari ya tafi ziyara a gabas ta tsakiya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bar Najeriya a jiya, Alhamis domin halartar wani taron tattalin arziki a babban birnin kasar Jordan Amman.


Sarkin kasar ta Jordan Abdullah II bin Al-Hussein ne ya gayyaci Shugaban domin shiga taron, kamar yadda fadar shugaban kasa ta sanar a wasu jerin sakonni a twitter.

Taron dai na tattalin arziki ne na duniya baki daya, wanda kuma zai mayar da hankali kan kasashen gabas ta tsakiya da kuma kasashen arewacin Afirka.

Yayin taron Shugaba Buhari zai yi jawabi tare da Sarki Abdallah da kuma Sakataren Majlisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, inda kuma zai hadu da sauran shugabannin kasashen duniya.

Daga bisani zai bar birnin Amman a ranar Lahadi zuwa Dubai, inda zai shiga wani taron zuba jari na shekara-shekara bisa gayyatar Sarki Sheikh Mohammed Bin Rachid Al Maktoum.


Shugaba Buhari zai gabatar da makala mai taken 'shimfida hanyar zuba jari domin habbaka tattalin arzikin duniya a zamanance' a yayin taron na Dubai.

Ana sa ran taron zai nemo hanyoyin zuba jari a kasashe sama da 140, wanda kuma zai sadar da huldar kasuwanci tsakanin kasashen da ke hulda da masu zuba jari.

Gwamnoni Badaru Abubakar na Jigawa da Abiola Ajimobi na Oyo da Yahaya Bello na Kogi na daga cikin wadanda za su yi wa shugaban rakiya.

Sauran sun hada da ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama da kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mejo Janar Mohammed Babagana Monguno.

Wannan na zuwa ne kwana biyu kacal bayan ya dawo daga kasar Senegal, inda ya halarci bikin rantsar da Shugaban kasar Macky Sall a karo na biyu.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment