Saturday, 13 April 2019

Shugaba Buhari zai je kasar Chadi

A yau, Asabar shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai halarci taron shuwagabannin kasashen yankin Sahel Sahara da zai wakana a kasar Chadi. Taron zai tattauna batutuwa  da suka shafo tattalin arziki tsaro da kuma zirg-zirga tsakanin membobin kasashen.Shugaba Buhari zai samu rakiyar gwamnonin jihohin Borno, Lagos da Osun da kuma wasu daga cikin mayan jami'an gwamnatin tarayya kamar yanda sanarwar da me magana da yawun shugaba  kasar, Malam Garba Shehu ya fitar ta bayyana.

Bayan kammala taron, shugaba Buhari zai dawo gida a yau Asabar in Allah ya yarda.

No comments:

Post a Comment