Thursday, 11 April 2019

Shugaban kasar Sudan Umar Albashir yayi murabus

Rahotannin dake fitowa daga kasar Sudan na cewa shugaban kasar, Umar Albashir ya sauka daga mukaminshi, hakan ya biyo bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati da 'yan kasar suka shafe watanni suna yi biyo bayan matsin tattalin arziki.Rahotanni daga gwamnatin kasar na cewa shugaba Umar Albashir na can an mai daurin talala a fadar gwamnatin kasar inda yake tsare tare da wasu manyan mukarraban gwamnatin nashi sannan ana shirin tsara wani kwamitin soji a kasar da zai karbi mulki daga hannun Albashir.

Albashir dai ya shafe shekaru 30 yana mulkin kasar da ya kwata ta hanyar juyin mulki wanda kuma kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya na nemanshi ruwa a jallo bisa aikata laifukan yaki a yankin Darfur, nan gaba kadanne ake sa ran sojin kasar zasu fitar da sanarwa a hukumance ta saukar Albashir daga mulki.

Tuni dai 'yan kasar da suka hada da matasa da mata dauke da 'ya'yansu, tike da tutar kasar a hannayensu suka fantsama akan tituna inda suke wakokin cewa sun yi nasara,ta fadi, masu gangamin murnar sun nufi ofishin sojin kasar inda suke tafi suna yaba musu.

No comments:

Post a Comment