Thursday, 4 April 2019

Tawagar El-Rufai ta fatattaki masu garkuwa da mutane


Governor of Kaduna State, Nasir El-RufaĆ¢€™i [Twitter/@GovKaduna]
Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya yi artabu da masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Laraba.


Masu tsaron gwamnan ne suka tarwatsa masu garkuwa da mutanen inda suka arce cikin daji.
Jami'i mai hudda da jama'a na gwamnan, Samuel Aruwan ne ya shaidawa BBC aukuwar lamarin.
Da aka tambaye shi ko hakan zai iya jawo wa jihar ja baya daga hannun masu saka hannun jari sai yace "Wannan shi ne karo na hudu da muke wannan taron, sha'anin tsaro abu ne mai fadin gaske"
Aruwan kuma ya bayyana cewa jami'an tsaron na gwamnan sun yi nasarar "bindige uku daga cikin masu garkuwa da mutanen."
Wannan na zuwa ne a lokacin da garkuwa da mutane a kan hanyar ta yi kamari inda a makon da ya gabata aka sace sama da mutum 40 a lokaci daya.
Mutanen da yawa na ci gaba da kauracewa hanyar inda suke hawa jirgin kasa domin gudun bacin rana.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment