Wednesday, 17 April 2019

Tsohon shugaban kasa ya harbi kansa da bindiga


Former Peruvian president Alan García
Tsohon shugaban kasar Peru Alan García ya harbi kansa da bindiga a lokacin da 'yan sanda suka je kama shi.


Asibitin Casimiro Ulloa da ke Lima, babban birnin kasar ya ce tsohon shugaban yana dakin tiyata inda ake cire masa harsashin da ke cikin kansa.
Ana zargin Mista García da karbar hanci daga wani kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht - zargin da ya sha musantawa.
An aika 'yan sanda su kama shi kan zarge-zargen da ake masa din.
Ministan lafiya Zulema Tomás ya ce Mista García na jin jiki sosai kuma yana cikin matsanancin hali, kuma sai da aka farfado da shi bayan da ya gamu da bugun zuciya har sau uku.
Lauyan tsohon shugaban kasar Erasmo Reyna ya shaida wa manema labarai a asibitin cewa: "Mu yi addu'a Allah Ya ba shi lafiya."
Mista García ya rike shugabancin kasar daga shekarar 1985 zuwa 1990 ya kuma sake daga shekarar 2006 zuwa 2011.
Masu bincike sun ce ya karbi hanci daga kamfanin Odebrecht a lokacin mulkinsa na biyu, da ke da alaka da gina wani layin jirgin kasa na zamani a babban birnin.
Kamfanin Odebrecht ya ce ya biya kusan dala miliyan 30 a matsayin cin hanci a Peru tun daga shekarar 2004.
Amma Mista garcia ya ce shi ne yake fuskantar bi ta da kullin siyasa, a wani sako da ya rubuta a shainsa na Twitter ranar Talata, yana mai karawa da cewa "babu wata shaida da ke nuna" ya aikata laifin.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment