Sunday, 14 April 2019

Tushen labarin Romeo da Juliet


Tushen labarin Romeo da Juliet
A Landan, babban birnin kasar Ingila,an gano ainahin cikakken adireshin inda shahararren sha'iri kana fitaccen marubucin labaran wasannin kwaikwayo,William Shakespeare ya rubuta labarin soyayyar "Romeo da Juliet".


A cewar kafar yada labarai ta kasar burtaniya BBC,an yi amfani da wasu hujjoji da sanannen masanin tarihin wasan kwaikwayo Geoffrey Marsh wajen gano ainahin inda Shakespeare’ ya rayu a Landan tsakanin shekarar 1597 da 1598.

Mrash wanda ya share shekaru 10 yana da gudanar da wannan binciken ya gano cewa, gidan Shakespeare na a unguwar Bishopsgate da ke gabashin birnin Landan kan titin Great St Helen's gida mai lamba 35.

A yanzu haka,a daidai inda ake kyautata zaton gidan Shakespeare marubucin labarin soyayyar Romeo da Juliet yake, wani wata ma'aikata.

Shakespeare ya kasance a sahun zakakurai a fagen adabi na kasar Ingila da ma duniya ga baki daya, sakamakon labaran wasan kwaikwayo 37 da kuma kasidoji 154 da ya rubuta,wadanda kawo yanzu ake ci gaba da amfani da su tamkar wasu taskokin sani.

An sanar da cewa, tsakanin shekarar 1585 da kuma 1612, Ba'ingilen marubucin ya rayu a wurare mabambanta.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment