Thursday, 11 April 2019

Wani matashi ya sha alwashin karbar bashin banki dan zuwa gurin Nafisa Abdullahi su yi wani abu

Soyayya takan sa mutum yayi abinda shi kanshi zai baiwa kanshi mamaki, musamman idan ya kamu sosai, kusan hakannne ke shirin faruwa da wani matashi da yace jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi na birgeshi.A sakon daya aika mata ta Twitter,yace ana girma ana rage kyau amma Nafisa kullun kara kyau kike, sai na amshi bashin banki dan inzo in ganki mu dauki hoto. Ban taba ganin mace me kyanki ba.

Nafisar dai tace ba fashin baki, hoto kawai.


No comments:

Post a Comment