Thursday, 11 April 2019

Wani yayi wa Kadaria Ahmad barazana akan cewa ta yi ridda: Ta mayar da martani

Wani mutum yayi zargin cewa shahararriyar 'yar jaridarnan Kadaria Ahmad ta karbi addinin kiristanci a Landan inda yace ya kadu da yaji cewa ita 'yar jihar Zamfarace. Ya kara da cewa a ka'idar addinin musulunci ita gawace.Ya kuma kara da cewa ya kamata ace an kasheta a matsayin wadda ta yi ridda.

Saidai Kadaria tace ta kai kararshi  saboda barazanar da yawa rayuwarta dan ba wani dake da ikon da zai ce a kashe mutum, kuma  idan wani abu ya sameta shine sanadi

No comments:

Post a Comment