Tuesday, 2 April 2019

Watakila mu kara kudin mai daga 145>>'Yan kasuwar Man fetur

Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta yi barazanar kara kudin man fetur daga 145 da aka saba saye saboda masu Depot suna sayar musu da man akan kudin da suka haura ka'ida.

Shugaban Ore Depot ya bayyanawa Punch cewa, masu Depot na zaman kansu na sayar musu da mai fiye Naira 133.28 wanda shine kudin ka'ida da gwamnati ta saka, yace idan basu daina sayar musu da man akan farashi sama dana gwamnati ba to dole suma su kara akan 145 da suke sayarwa da mutane.

No comments:

Post a Comment