Wednesday, 3 April 2019

Wolverhampton ta ci Man United 2-1

Wolverhampton ta yi nasarar doke Manchester United da ci 2-1 a wasan mako na 33 a gasar cin kofin Premier da suka kara a Molineux ranar Talata.


United ce ta fara cin kwallo ta hannun Scott McTominay minti na 13 da fara tamaula, sai dai Wolves ta farke ne ta hannun Diogo Jota a minti na 25.

Wolves ta samu damar kara kwallo na biyu ne, bayan da United ta ci gida ta hannun Chris Smalling, bayan da aka bai wa Ashley Young jan kati kan keta da ya yi sau biyu a wasan.

A karawar farko da kungiyoyin biyu suka buga a Premier bana sun tashi ne 1-1 a Old Trafford ranar 22 ga watan Satumba 2018.

Haka kuma Wolves ce ta yi waje da United da ci 2-1 a FA Cup na bana a karawar da suka yi ranar 16 ga watan Maris din 2019.

Rashin nasarar da United ta yi a hannun Wolves ranar Talata ya sa kungiyar tana ta biyar a kan teburin Premier da maki 61, ita kuwa Wolves tana ta bakwai da makinta 47.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment