Tuesday, 30 April 2019

Ya saci na'urar miliyan 1.7 ya sayar da ita Naira dubu 5

'Yansanda a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina sun damke wani Hamza Sani dan shekaru 30 bisa zargin hada hannu da wasu mutane dan sace na'urar bincike mallakin babban asibitin garin Malumfashin.Rahotanni sun nuna cewa, Sani ya sayar da na'urar da kudinta suka kai Miliyan 1.7 akan Naira dubu 5 kacal.

Asirin Sani ya tonune bayan kama abokan huldarshi kuma ya amsa laifinshi inda yace ya sayar da na'urar naira 5000 ne dan yiwa matarshi da bata da lafiya magani.

No comments:

Post a Comment