Thursday, 11 April 2019

'Yan bindiga na iko da wani yankin jihar Katsina>>Gwamna Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyanawa shugaban 'yansandan Najeriya, Muhammed Adamu cewa akwai fa yankunan jihar dake karkashin ikon 'yan bindiga.Gwamnan wanda mataimakinshi, Mannir Yakubu ya wakilta ya bayyana cewa, ya gana da shuwagabannin kananan hukumomi 8 da suka fi fuskantar matsalar 'yan bindigar da satar mutane inda ya bukaci su tashi tsaye dan aiki tare wajan kawar da wannan matsala.

Gwamnan ya kuma tabbatar da bayar da gudummawarshi ga yakin da hukumomin tsaron ke yi da 'yan bindigar inda yace ya bayar da guraren kwana da kayan masarufi da motoci 12 ga 'yansandan dan ganin an samu nasarar wannan aiki. Gwamnan ya bayar da labarin cewa 'yan bindigar na cin karensu babu babbaka inda har gida-gida suke bi wajan satar mutane dan kudin fansa inda ya bayar da misali da surukarshi da aka sace kwanakin baya.

Kananan hukumomin Jibia, Batsari, Safana, Dan-Musa, Faskari, Sabuwa, Dandume  da Kankara ne suka fi fuskantar wadannan matsaloli saboda wasu daga cikinsu na iyaka da jihar Zamfara inda lamarin yafi kamari.

No comments:

Post a Comment