Sunday, 7 April 2019

'Yan kudu ku manta da maganar karba-karba a 2023>>Junaidu Muhammad

Tsohon dan majalisar wakilai a jamhuriya ta biyu, Junaidu Muhammad ya bayyana cewa a zaben shekarar 2023 me zuwa babu maganar cewa wai a yi karba-karba kawai duk yankin da ke da karfin siyasa ya fito da dan takara.A hirar da yayi da The Sun, Junaidu ya bayyana cewa a baya an yi tsarin na karba-karba amma be haifar da 'da me ido ba to dan me za'a yi ta yin abu daya sannan kuma ayi tsammanin samun sakamako na daban?

Ya caccaki kungiyar Ohanaeze ta yankin Inyamurai inda yace sun karbi kudin Atiku suka yishi, yace siyasa ba kasuwanci bace, abune da ya kamata a daukeshi da muhimmanci, kuma kuri'un Inyamurai na zaben 2023 ya nuna cewa su siyasar kabilanci suke yi dan haka babu wanda zai zabi dan takararsu, ya kara da cewa ta yaya mutum zai yi tunanin fitowa gidajen jaridu kana zagin mutane shi zai sa su zabe ka?

Yace akawai kabilu da dama a kasarnan, kuma siyasa yimin in makane amma idan kace kai kanka ka sani to babu wanda zai tafi tare da kai, yace za'a zura ido aga wane dan takara Inyamuran zasu goyi baya kuma a 2023?

Ya kuma ce suma yankin Yarbawa da suke ta wani hankoron cewa 2023 lokacinsune su yi mulki, ba haka abin yake ba, kawai yankin da yafi karsashin siyasane zai tsayar da dan takara.

No comments:

Post a Comment