Saturday, 6 April 2019

'Yan kwallo 10 da suka fi iya cin kwallo da Free-kick: Babu Ronaldo da Messi a ciki

Taurarin kwallon kafa, Cristiano Ronaldo da Lionel Messi basa cikin 'yan kwallo 10 da suka fi iya cin kwallo daga tazara me nida da shinge ba watau, Free-kick a turance ba.Jadawalin sunyen 'yan kwallo 10 da Givemesport suka fitar jiya, Juma'a da sune suka fi iya cin kwallo da Free-kick a tarihi sun fara da sunan Juninho Pernambucano wanda yaci kwallaye har 77 da Free-kick kamin yayi ritaya a shekarar 2013.

Me biye mai shine Pele da yaci kwallaye 70 da Free-kick.

Ronaldo yaci kwallaye 53 da free-kick yayin da shi kuma Messi yaci 47.

Ga sunayen 'yan kwallon da suka fi iya cin kwallo da Free-kick a tarihi:

1. Juninho – 77 goals

2. Pele – 70 goals

3. Legrottaglie – 66 goals

4. Ronaldinho – 66 goals

5. Beckham – 65 goals

6. Maradona – 62 goals

7. Zico – 62 goals

8. Ronald Koeman – 60 goals

9. Ceni – 59 goals

10. Carioca – 59 goals.

No comments:

Post a Comment