Monday, 1 April 2019

Yanda muka yi rayuwa a hannun masu garkuwa da mutane da yanda muka tsira>>Alaramma Ahmad Sulaiman

A hirarshi da jaridar Daily Trust, Alaramma Ahmad Sulaiman ya bayyana yanda masu satar mutane dan kudin fansa suka saceshi akan hanyarshi ta dawowa Kano daga Jihar Kebbi inda yaje gaisuwa. Yace wanda yake tare dasu lokacin da aka saceshi 'ya'yanshine sai 'yan uwa, dama can haka suka saba yin tafiya.
Malam yace gaisuwace yaje yi jihar Kebbi to saboda a gidan gwamnatine saida sukai ta neman samun damar ganawa da matar gwamnan jihar wanda suka jima basu samu ba, daga baya aka basu dama kuma suka yi sammako suka tafi Kebbin, ranar Alhamis, 14 ga watan Maris.

Malam yace akwai 'ya'yanshi 3 da zai aurar gab da saceshi da aka yi.

Ya kara da cewa da yake motarsu bata da lafiya sosai ta rika basu matsala, su kaita tsaye-tsaye a hanya, hakan yasa basu isa Kebbin da wuri ba, sun gama gaisuwa suka kuma kamo hanyar dawowa yayin da duhu yayi, muna cikin tafiya akan haryar tsakanin kauyen Kakumi da Kankara, jihar Katsina sai suka fito sanye da kayan sojoji suka fara harbi, har suka samu motarmu, sun fito damu daga mota suka dake mu suka tattakamu. Da farko sun amshi dubu dari 5 sukace mu tafi amma daga baya suka yanke shawarar yin garkuwa damu, Inji Malam.

Yace sun yi ta tafiya cikin daji a kafa har gari ya waye sannan suka daukesu akan mashina zuwa wani guri dake da bukka wadda da rarrafe ake shiga cikinta, haka suka shiga a ciki sukaita ajiyarsu.

Malam ya kara da cewa basu samu matsalar abinci ba, an rika kawo musu shinkafa da wake da mai, shine ma da yayi korafin yana da matsalar rashin lafiyar ciki suka rika kawo mai koko. Yace, sun hanamu muyi wanka amma daga baya sun barni na rika wanka sau uku a rana, yace sun yi ta musu barazana kala-kala da kuma cewa zasu kashesu idan ba'a kawo kudin fansa ba tunda 'yan wansu basu damu dasu ba.

Malam ya kara da cewa suna barinshi yayi ta karataun Kur'ani da addu'o'i, abinda baya samun damar yi lokacin yana gida, sannan kuma suna barinsu su yi sallah, sune ma suke fito dasu idan lokacin sallah yayi suce su fito su yi sallah, yace amma su basa yin Sallah sai yaro daya daga cikinsu wanda yake binsu jam'i, kuma idan suka yi sallah baya nan, idan ya dawo zai yi tashi. Fulatanci suke yi, sai idan zasu yi magana da mune sai su yi mana da Hausa, yaronnan da muke sallah dashi ya ce min in rika mai addu'a Allah yasa ya daina abinda yake, basu yi mana wani abuba in banda wani shakiyin yaro da ya taba marina, inji malam.

Sannan na lura cewa akwai wanda basa jin dadin abinda ke faruwa, suna kukan cewa rashin shanu da filin nomane da kuma idan suka shigo gari yanda ake hantararsu yasa suka shiga wannan sana'a. Daga baya sun shiga firgici har suka ce mu rika sakasu a addu'a kada dalilinmu azo a kashesu, wani daban ya zo inda muke ya zazzageni sannan yace idan ya sake dawowa sai ya kakkarya min kafafu, inji Malam.

Saidai hakan ya kawo rikici tsakaninsu, dan wanda muke tare dasu sukace ba zasu barshi ba tunda ba shine ya sato mu ba, hakan har fada ya jawo tsakaninsu wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu. Sun shiga firgici sosai, kuma hakan baya rasa nasaba da addu'o'in da muke yi da wanda ake mana daga gida, na yi ta tunanin me ya hana mutanena su yi gaggawar samo kudin fansar su biya dan a sakemu, watakila dan basu san halin da muke ciki bane, malam ya kara da cewa, saidai ashe jami'an tsaro suna nan anata fafutukar yanda za'a kwatomu.

Sun riga gaddama tsakaninsu ta cewa a kashe mu, wasu na cewa kada a kashemu saboda zasu samu kudi sosai damu, sannan wasu cikinsu sun rika cewa ko an kawo kudin fansar sai sun kashemu.

Wata rana muna zaune sai suka zo suka ce ga wasu nan daga cikin mutanensu suna so su sace mu daga gurinsu, wannan yasa aka hadamu da wasu mutane biyu wanda basu da makami suka tafi damu wata maboya ta daban, da zummar cewa idan mutanen nasu sunzo sai su nuna mana hanyar da zamu bi mu gudu.

To ashe jami'an tsarone suka zo da mahaifiyar shugabansu da aka kama wadda aka yi musayar ta damu, yanda aka yi muka kubuta kenan, naji ance an basu miliyan 33 wanda bama su cika ba.

No comments:

Post a Comment